Manyan mgoya bayan jam’iyyar PDP da dama ne a Jihar Legas suka tabbatar da ficewarsu daga cikinta tare da ayyana jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar da suka koma.

Daga cikin waɗanda suka fice daga jam’iyyar ta PDP a Legas ciki harda kakakin jam’iyyar na Jihar Hakeem Amode.
A taron manema labarai da kakakin jam’iyyar ta PDP a Legas ya yi a yau Litinin, ya sanar da ficewarsa daga cikin jam’iyyar da kuma komawa APC.

A yayin taron Amode tare da wasu manyan shugabanni a jam’iyyar ne suka sanar da ficewarsu daga cikinta.

Acewar Amode shi da sauran masu sauya sheƙar sun samu ƙwarin gwiwa ne daga Abdul-Azeez Adediran wanda ya kasance ɗan takarar gwamnan a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, inda a halin yanzu shi ma yana cikin jam’iyyar ta APC.
Sannan a halin yanzu jam’iyyar PDP tun daga kan matakin Ƙasa har zuwa Jiha sauya daga kan dukkan tsare-tsaren da aka kafa ta.
