Mutane biyu da su ka haɗa da makiyaya ne su ka mutu yayin wani hari da aka kai a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Sannan akwai wasu mutane biyu da su ka samu munanan rauni wanda aka kai su asibitin koyarwa na jami’ar Jos a jihar
An kai harin ne a Uwok-Ishe da ke gundumar Kakkek a ƙaramar hukumar Bassa ta Plateau da misalin karfe 7pm na daren jiya Lahadi.

Wani mai suna Abubakar Abdullahi mazaunin unguwar ya ce mutanen shidan da lamarin ya rutsa da su na haye kan babura biyu.

Akwai Fulani uku da kabilar Bache wato Rukuba.
Zuwa yanzu jami’an tsaro ba su ce komai dangane da lamarin ba.
