Akalla magoya bayan jam’iyyar Labour Party 10,000 ne a Jihar Enugu suka sauya sheka daga jam’iyyar zuwa Jam’iyyar APC.

Daga cikin masu sauya shekar ciki harda wasu shugabannin jam’iyyar ta Labour da suka harda da ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar Udi da Ezeagu Hon Sunday Umeha, da sauran manyan jagororin Jam’iyyar.

A wani taro da suka gudanar kan sauya shekar jagororin jam’iyyar suka tabbatar da barin Labour zuwa APC.

Umeha ya bayyana sun koma APC ne domin su goyi bayan shugaba Tinubu a zaben 2027 da ke tafe, kuma sun goyi bayan shi ne bisa yadda ya ke kokarin ganin ya gyara Najeriya.

Sannan ɗan Majalisar ya kuma yaba da irin jajircewar shugaba Tinubu wajen samar da ababan more rayuwa a Jihar Enugu don ganin Jihar ta ci gaba.

A yayin taron shugabannin jam’iyyar APC na jihar ne suka tarbi masu sauya sheƙar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: