Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Rivers Chief Tony Okocha ya bayyana cewa ya zama wajibi dakataccen gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara ya rungumi sulhu matukar yana son komawa kan kujerarsa.

Shugaban ya bayyana hakan a yau Talata a birnin tarayya Abuja a ganawarsa da manema labarai.
Shugaban ya ce tun bayan dakatar da Wike daga kan kujearsa ta Gwamna da shugaba Bola Tinubu yayi, har yanzu Fubara bai yi wata yin yukurin yin sulhu ba da ‘yan majalisar dokokin Jihar.

Okocha ya kara da cewa matukar Fubara ya rungumar yin sulhu na gaskiya, hakan ne kawai zai kubtar dashi daga rasa kujerarsa ta gwamna, duba da cewa har yanzu hukuncin kotun koli ya na nan.
