Kungiyar SERAP a Najeriya ta bukaci shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya dakatar da ministan birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike bisa barazanar da yayi na kulle ofisoshi 34 na jakadancin ƙasashen ketare da ke birnin tarayya Abuja.

A wata sanarwa da Kungiyar ta fitar a jiya Litinin, ta bukaci shugaba Tinubu da ya bai’wa Wike umarnin janye aniyarsa ta kulle ofisoshin.

Sanarwar ta kara da cewa matakin na Ministan ya sabawa sashi na 22 (1) na yarjejeniyar da aka kulla kan ofisoshin jakadancin Ƙasashen waje.

Kungiyar ta ce matukar ya dauki matakin rufe ofisoshin haka ya saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa.

Adon haka kungiyar ta bukaci shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya gaggauta dakatar da Wike daga wannan mataki da yake shirin dauka.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: