A gobe Alhamis 12 ga watan Yuni ake sa ran shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai cire dokar ta ɓaci da ya ƙaƙaba a jihar Rivers.

An saka dokar ne bayan gaza samun daidaito tsakanin gwamnan jihar da ƴan majalisar dokokin jihar.


Shugaba Tinubu ya dakatar da gwamnan da mataimakiyarsa da yan majalisar dokokin jihar baki ɗaya.
Sai dai a wani bayani da Matashiya TV ta samu ta jiyo akwai ƙishin ƙishin cewar shugaban na iya ɗage takunkumin a gobe.
A gobe 12 ga watan Yuni ke kamawa shekara 26 ana mulkin Demokradiyya a Najeriya.