Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen samun hadari da ruwan sama tsawon kwanaki uku.

 

Za a fara samun hadar da ruwan saman daga yau Laraba.

 

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce a wasu yankunan jihohin Taraba, Kaduna da Adamawa za a fara samun yanayin a safiyar yau.

 

Sai kuma tsawa da za a samu a jihohin Kano, Bauchi, Gombe, Kaduna, Zamfara, Katsina, Taraba da Sokoto da za a samu zuwa yammaci.

 

Haka kuma a birnin tarayya Abuja da Kwara, Benue, Niger da Nassarawa za a samu tsawa.

 

Sai kuma hasashen samun ruwan sama a jihohin Niger, Nassarawa, Kogi, Kwara, Plateau da Abuja.

 

Ko da cewar za a samu washewar sararin samaniya a jihohin Ondo, Ekiti da Ondo.

 

Sai dai daga bisani za a iya samun ruwan sama da tsawa a Imo, Enugu, Abia, Ebonyi, Anambra, Ondo, Oyo, Ogun, Ekiti, Edo, Delta, Bayelsa, Cross River, Akwa Ibom da Rivers.

 

A safiyar ranar Juma’a za a iya samun tsawa a jihohin Jigawa, Gombe, Bauchi, Adamawa da Taraba.

 

Hukumar ta shawarci mutane da su kaucewa tsayawa kusa da bishiya don kaucewa faduwarsu.

 

Haka kuma ta shawarci masu jiragen sama da su inga bibiyar hasashen yanayi na musamman da ake bai wa filin jirage.

Leave a Reply

%d bloggers like this: