Kotun Koli a Najeriya ta tabbatar da gwamnan Jihar Edo Monday Okpebholo a matsayin zaɓaɓɓan gwamnan Jihar Edo karkashin inuwar jam’iyyar APC bayan zaben shi da aka yi tun a wata Satumba shekarar 2024 da ta gabata.

Kotun mai kwamitin Alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a Mohammed Garba ta yanke hukuncin a yau Alhamis, inda kotun ta kawo karshen shari’ar da ake yi akan kujerar gwamnan.

A yayin yanke hukuncin kotun ta yi fatali da bukatar ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a Jihar Asue Ighodalo da jam’iyyarsa da su ka shigar gaban kotun, inda kotun ta bayyana hujjojin dan takarar gwamnan na PDP a matsayin marasa inganci.

Kotun ta kara da cewa masu shigar da karar ba su gabatar mata da gamsassun hujjojin da za ta aminta da su ba, akan nasara gwamna Monday da kuma rashin bin doka a lokacin zaben.

Kotun ta ce rashin gamsassun hujjojin ne ya sanya ba za ta soke zaben gwamnan Jihar ta Edo ba kamar yadda masu shigar da kara suka nema.

Leave a Reply

%d bloggers like this: