Sashen Hausa na kwalejin ilmi ta Aminu Kano AKCOE hadin guiwa da jami’ar tarayya ta dutsin-ma da ke jihar Katsina ya ciri tuta, a tsakanin sauran sassan kamakantar.

Shugaban kwalejin Dakta Ayuba Ahmad Muhammad ne ya bayanna hakan, a wajan taron Ga Fili Ga Mai Doki da sashen Hausan ya hada a karshen makon jiya.
Ya ce, sashen sun san me su ke yi duba da yadda gogaggu kuma kwararrun makamai ke koyarwa a sashin hakan ya sa su ke da jajirtattun dalibai kuma hazikai.

A nasa jawabin Turakin Kano hakimin Gwale, bukata ya yi da al’umma su fara sanin kan su kafin su yi kokarin sanin wani abu, a ruyuwar su wanda ta haka ne, za su sami cigaban da ya dace.

A nasa bangaren farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, bayyana cewa ya yi ana shirya taron ne don a fadi ka’idoji da sharudda da ya kamata a yi waka ta furuci a kuma yi kida a sadar da shi ga al’umma.
Shi kuwa makadin da ya gafarta da kida a wajan Alhaji babangida kakadawa cewa ya yi, dama yanayin wakokinsa ne, don ilmantarwa da fadakarwa da kuma wa’azantarwa.
Dr Mahe Isah Ahmad shi ne shugaban sashen, na Hausa a makanatar ya ce taron ba iya na dalibai ba ne, na duk wani mai kishin Hausa ne.
Taron dai shi ne karon farko a tarihin kafuwar makarantar wanda sahin Hausar ya hada karkashin jagorancin malamin da ke koyar da darasin Musa Labaran da hadin guiwar kungiyar daliban Hausa ta makarantar ƙarƙashin jagorancin kwamared Abubakar Sabo.
