Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kudurin dokar gyara kamfanonin inshora na Najeriya.

Fadar shugaban kasar ta ce kudirin dokar wata muhimmiyar doka ce don karfafa bangaren hada-hadar kudi ta Najeriya da kuma tafiyar da al’ummar kasar zuwa ga tattalin arzikin dala tiriliyan 1.
Bayo Onanuga mai bai’wa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Ya ce dokar sake fasalin masana’antar inshora ta Najeriya a 2025 ta soke tare da daidaita wasu tsoffin dokokin inshora zuwa tsarin doka guda daya na zamani.

Ya ce sabuwar dokar ta tanadi cikakken tsari da sanya ido kan duk wani kamfani na inshora da inshorar da ke aiki a Najeriya.
A cewarsa wannan ci gaban ya sake tabbatar da kudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da daidaiton harkokin kudi, bunkasar tattalin arziki, da kuma ci gaban.
