Kungiyar tsaffin ‘yan majalisar dokokin Jihar Kebbi sun amincewa da salon mulkin gwamna Nasir Idris, bisa kwazon wajen gudanar da mulkinsa cikin shekaru biyu da yayi akan karagar mulki.

Kungiyar ta bayyana goyan bayanta ga gwamnan Idris ne a wata ziyara da ta kai masa a jiya Litinin.

Shugaban kungiyar kuma tsohon kakakin majalisar Hassan Shalla, ya ce gwamnan ya samar da abubuwan ci gaba, tare da ingata jihar ta fannoni daban-daban.

Acewar Shalla ya birnin jihar ya samu sauyi sosai karkashin jagoranci gwamnan Nasir Idris.

Shugaban ya ce Juhar Kebbi ta samu ci gaban da tun daga kan aikin gina titina, bangaren kiwon lafiya, ilimi, da sauran wasu bangarorin.

A nasa martanin gwamna Idris ya nuna jin dadinsa da hadin kai da suka ba shi, ya kuma bayyana amincewa da hakan a matsayin wani kwarin gwiwa ga gwamnatinsa.

Ya kuma yi kira ga tsofaffin ‘yan majalisar da masu ruwa da tsaki a jihar da su ci gaba da bai’wa gwamnatinsa goyon baya a kokarin da suke yi na ciyar da jihar ta Kebbi gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: