An tabbatar da rasuwar mutane takwas yayin da aka yi asarar gonaki 800 a wata ambaliyar ruwa da ta lalata gonaki a Enohia, da ke ƙaramar hukumar Afikpo a jihar Ebonyi.

Shugaban ƙaramar hukumar Afikpo Hon. Timothy Nwanchi ya tabbatar da lamarin tare da jajantawa mutanen da ain ya shafa.
Haka kuma ya sha alwashin ɗaukar matakan da su ka dace don ganin hakan ba ta sake faruwa ba.

Nwanchi ya roƙi mutanen da su ke zaune a unguwar da ambaliyar ta afku da su tashi su koma inda zasu tseratar da kansu daga faruwar ambaliyar, domin yawan ruwan saman da ke sauka zai iya kawo ambaliyar a unguwar da suke zaune.

Ya ce bai ji daɗin iftila’in da ya faruwa ba har ma ya jajanta musu tare da ta’aziyyar mutane da su ka rasu.
Ya ƙara da cewa a matsayinsu na shugabanni, za su haɗa kai da masu ruwa da tsaki a jihar da ma tarayya domin kawo musu agaji da kuma rage raɗaɗi ga waɗanda abin ya shafa.
Akarshe ya buƙaci mutanen da ke zaune a ƙaramar hukumar da su tabbatar da sun yashe magudanan ruwan su domin kaucewa toshewar magudanan ruwan.
