Minister babban birnin tarayya Abuja Nyesome Wike ya gargadi yan jam iyyar PDP akan yunkurin su na dawo da tsohon dan takarar shugaban kasa dake jam iyyyar Labour Party Peter Obi cikin jam iyyar PDP.

Yayin da yake maganar a kafar yada labarai ranar Litinin, ya ce jam’iyyar PDP ba ta ɗauki darasin kuskuren abinda ya faru ba a lokacin zaɓen shekarar 2023.

Ya ce da shi da sauran shugabannin jam iyyun sun ja hankali a kan barin tsohon dan takarar shugaban ƙasa kuma shugaban jam iyyar ya fito daga yankin arewa bai dace ba kuma zai kashe jam iyyar a siyasance.

Ya ƙara da cewa daga ranar farko ya fadawa abokan siyasarsa na cikin jam’iyyar PDP cewa su na cakawa kansu wuƙa idan har su ka cigaba da sa ido akan abin da ke faruwa ya cigaba. Ya ce ba zai yu a samu ɗan takarar shugaban ƙasa ba da kuma shugaban jam iyyar a lokaci daya duka daga yankin arewa.

Tsohon gwamnan jihar Rivers ya zargi jam iyyar PDP da yin burus wajen yin adalci da samar da daidaito wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa ƙuri’un da jam iyyar ta yi.

Wike ya jaddada cewa dole tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya fito daga yankin kudanci domin samar da adalci a siyasar, ya ce rashin daukar magana da ƴan jam iyyar PDP ne yasa jam iyyar ta samu koma baya.

Ya kuma yi watsi da dawowar Obi izuwa jam iyyar PDP tare da misalta hakan a matsayin ganganci da munafurci.

Ya ce shigowarsa ce za ta zubar da ƙima tare da rushe ginin da jam iyyar ta jima ta na yi.

Wike ya ce zai tsaya tsayin daka domin tabbatar da adalci da daidaito a shiyyar tasu kuma za ta kasance wajen da jam iyyar PDP za ta riƙe mutuncin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: