Gwamnatin Tarayya ta yi Allah-wadai tare da ƙaryata zarge-zargen da wasu kafafen watsa labarai na ƙasashen waje da masu tasiri a kafafen sada zumunta suke yi na cewa wai ‘yan ta’adda a Nijeriya suna yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Gwamnatin ta ce irin wannan iƙirarin “ƙarya ne, marasa tushe, abin ƙyama, kuma na raba kawuna.”

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce: “Bayyana matsalolin tsaro a Nijeriya a matsayin wani yaƙi da aka kitsa musamman kan wasu mabiya addini guda ɗaya ba daidai ba ne, kuma rashin adalci ne.”


Ya ƙara da cewa: “Ko da yake Nijeriya, kamar dai wasu ƙasashen, tana fuskantar matsalolin tsaro, ciki har da ta’addanci da ‘yan ta’adda suke aikatawa, fassara wannan a matsayin wani hari na musamman kan Kiristoci ba gaskiya ba ne, illa ma cutarwa ne.
“Hakan na wofintar da matsala mai matuƙar rikitarwa, kuma yana taimaka wa ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifi wajen raba kan ‘yan Nijeriya bisa addini ko ƙabila.”
Idris ya ce: “Ayyukan ta’addanci ba su taƙaita ga wata al’umma ta addini ko ƙabila ɗaya ba. Waɗannan miyagun suna kai hari ga duk wanda ya ƙi bin aƙidar su ta kisa, ko Musulmi, ko Kirista, har ma wanda ba ya bin wani addini. Duk suna shan wahala a hannun su.”
Ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya tana da cikakken ƙudirin murƙushe ƙungiyoyin ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, kuma wannan tuni aka riga aka fara ganin sakamakon sa.
Ya ce: “Tsakanin watan Mayu na 2023 da Fabrairun 2025 kaɗai, an hallaka ‘yan ta’adda da masu laifi sama da 13,543 tare da kuɓutar da kusan mutum 10,000 daga hannun su a faɗin ƙasar nan. A watan da ya gabata ma, an cafke manyan shugabannin ƙungiyar ANSARU, ƙungiyar da ke da alaƙa da Al-Ƙa’ida, a wani babban samamen yaƙi da ta’addanci. Sun haɗa da Mahmud Muhammad Usman (wanda aka fi sani da Abu Bara’a/Abbas/Mukhtar), wanda ke kira kan sa Sarkin ANSARU, da kuma Mahmud al-Nijeri (wanda aka fi sani da Malam Mamuda), wanda ya kasance mataimakin sa.”
Ministan ya ce waɗannan nasarorin wata hujja ce ta jajircewar jami’an tsaro da kuma rashin ingancin zargin cewa Nijeriya tana lamunta da ta’addancin da ya ta’allaƙa da addini.
Ya ƙara da cewa: “Gwamnatin Tarayya ba ta yi ƙasa a gwiwa ba a aikin ta na kare kowane ɗan Nijeriya, ba tare da la’akari da addini ko ƙabilar sa ba. Rundunar Sojojin Nijeriya da ta ‘Yan Sandan Nijeriya kuma suna gudanar da kotunan soja da shari’o’i don hukunta jami’an da suka karya doka. Wannan na nuni da muhimmancin ladabi da bin doka a hukumomin tsaro.”
Ya jaddada cewa Nijeriya ƙasa ce mai addinai da dama, wadda ke ɗauke da manyan al’ummomin Musulmi da Kiristoci a duniya. “Kiristanci ba ya cikin haɗari ko kuma ana nuna masa wariya a Nijeriya,” in ji shi.
Ya kuma yi nuni da cewa: “Shin waɗannan masu saka baki daga ƙasashen waje sun san cewa manyan hafsoshin Rundunar Sojojin Nijeriya da ‘Yan Sandan Nijeriya a yanzu dukkansu Kiristoci ne? Wannan kansa na nuna yadda jagorancinmu ya kasance na haɗin kai.”
Game da yaƙi da ta’addanci, Ministan ya bayyana cewa an yi nasarar gurfanar da wasu ‘yan Boko Haram a gaban kuliya: “Zuwa yanzu, an yi nasarar gurfanar da rukuni bakwai na waɗanda ake zargi, inda aka samu hukunci sama da 700. A yanzu muna shiga zagayen takwas na shari’ar, don nuna tsananin ƙudurinmu wajen yaƙar ta’addanci da masu ɗaukar nauyinsa.”
A cewarsa, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙari don tabbatar da adalci da ƙara tsaro.
“Labarin Nijeriya ba na kisan ƙare dangi na addini ba ne. Labarin ƙasa ce mai juriya, bambance-bambance, da ƙuduri na haɗin kai wanda duniya ta shaida.”
Ya tuna cewa a watan Maris na bana, lambar yabo ta farko ta Commonwealth Peace Prize an bai wa shugabannin addinai biyu na Nijeriya — Fasto James Movel Wuye da Liman Muhammad Nurayn Ashafa — saboda aikinsu na gina amana da haɗin kai tsakanin Musulmi da Kiristoci.
Ya ce: “Wannan na nufin cewa Nijeriya ba wai kawai tana fitar da al’adu da kiɗa zuwa duniya ba ne, har ma tana fitar da tabbataccen tsari na musamman na zaman lafiya tsakanin addinai.”
A ƙarshe ya yi kira ga kafafen watsa labarai na duniya da masu sharhi su guji rashin sani da yin tashe-tashen hankula ta hanyar kalaman rarraba kawuna. “Maimakon haka, ya kamata a tallafa wa ƙoƙarin Nijeriya na ci gaba da yaƙar ta’addanci da duk wani irin laifuka,” inji shi.