Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta bukaci majalisar dokoki ta ƙasa da ta gaggauta amincewa da sabbin dokokin da a ka gabatar mata

 

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana haka jiya Alhamis a yayin ganawa da tawagar sa jdo a kan zaɓe na tarayyar turai da su ja kai masa ziyara.

 

Shugaban ya jaddada cewa amincewa da sabbin dokokin a kan lokaci zai taimakawa hukumar don fara gudanar da shirye-shirye a kan lokaci gabanin babban zaɓen 2027.

 

Daga cikin sabbin dokokin da su ke so a amince da su akwai, zaɓen wuri, zaɓen ƴan Najeriya mazauna ƙetare, gyara amfani da katin zaɓe na dindindin, bai wa INEC damar naɗa kwamishinonin zaɓe na jihohi da samar da hukumomin sasanta rikicin zaɓe.

 

Farfesa Mahmud Yakubu ya ce hukumar ta ɗauki matakai a kan waɗanda ke buƙatar sauye-sauye na cikin gida, kuma ta na aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki a kan shawarwari da su ka shafi kowa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: