Gwamnatin Tarayya ta sake ƙaryata zargin da wani Sanatan ƙasar Amurka wai shi Ted Cruz ya yi cewa wai ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya ƙaryata zargin a cikin wata hira ta musamman da Fox News Digital da ke Amurka ta wallafa a ranar Talata.

Ministan ya ce: “Gwamnatin Nijeriya ta ƙi amincewa da wannan zargi. Wannan ba gaskiya ba ne kwata-kwata.”

Yayin da yake mayar da martani kan alƙaluman da Sanata Cruz ya bayar, Idris ya ce: “Ba gaskiya ba ne. Wannan ba shi ne abin da ke faruwa ba. Ina nufin ba gaskiya ba ne a ce an ƙone fiye da coci 20,000. Kuma ƙarya ce a ce an kashe Kiristoci 52,000. Daga ina ya samo waɗannan alƙaluma? Ba shi da wata hujja ko shaidar da ya dogara da ita. Gwamnatin Nijeriya ta ƙi amincewa da wannan zargi.”

Ya kuma jaddada cewa babu wani jami’in gwamnati ko wata hukuma a Nijeriya da ke mara wa ‘yan ta’adda baya ko yin aiki tare da su don kai hari ga mabiya wani addini.

A cewar sa: “Babu wani jami’in gwamnati a Nijeriya da zai goyi bayan masu tayar da ƙayar baya don su kai hari ga mabiyan wani addini. Wannan zargi ƙarya ne ɗari bisa ɗari.”

Ministan ya sake tabbatar da cewa Nijeriya ƙasa ce mai yawan addinai da kuma zaman lafiya da juna, inda ya ce: “Nijeriya ƙasa ce da ke da mabiya addinai daban-daban. Muna da Kiristoci, muna da Musulmai, har da waɗanda ba sa bin waɗannan addinai biyu. Nijeriya ƙasa ce mai yarda da bambancin addinai. Gwamnatin Nijeriya ta ƙudiri aniyar tabbatar da cewa ana da ‘yancin yin addini a ƙasar nan.”

Ya ƙara da cewa matsalar ta’addanci ta shafi kowa, ba tare da la’akari da addini ba. Ya ce: “Abin baƙin ciki ne cewa waɗannan ‘yan ta’adda suna kashe Kiristoci da Musulmai a wurare daban-daban da suke samun goyon baya. Don haka, ba gaskiya ba ne. Gaba ɗaya ƙarya ce a ce wai ana da wani shiri ko ƙudiri na gangan don hallaka wata ƙungiyar addini; wannan ba daidai ba ne, abin takaici ne ƙwarai.”

Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya tana da cikakken ƙudirin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, inda ya jaddada cewa hukumomin tsaro na ƙasar nan ba su yi ƙasa a gwiwa ba a yaƙi da ta’addanci da fashi da makami a kowane salo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: