
Duk da cewar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na Kasa kuma Mataimakin Kakakin Majalisar Raya Kasashen Afirka Ta Yamma, (ECOWAS Parliament) Sanata Barau Jibrin ba mutum ne mai taskance kansa ga mazabarsa ba kawai, har yanzu dai ya yarda cewar hidimtawa al’umma gaba daya shine babban burinsa.
Maganar gaskiya kuma ita ce, ba wanda yake tantamar cewa, su wadanda su ka taskance kansu ga mazabarsu kawai, ba mutane ne masu muhimmanci a tafiyar jam’iyyar APC a jihar Kano ba.

Amma babban abin lura din shine, shi a wajen Barau, bayan cewar ya yarda da tushe, wato mazabarsa da yake wakilta a majalisar dattawa, a wajen sa, hada hannu da hannu da wadanda ya dace a jiha babban abu ne. Kuma yin alaka ta kut-da-kut da jagorori a matakin kasa, har ta kai masa samun tagomashi a wannan nahiya ta mu ta Afirika Ta Yamma da kuma sassan duniya, babbar manufa ce da ya kamata a sa a gaba.

Daga lokacin da a ka zabi Sanata Barau a matsayin, mataimaki na farko na ECOWAS Parliament, lokacin da a ke gabatar da majalisar a karo na 6, a Abuja, daga nan ne fa ya kara samun tagomashi a idon duniya.
Kuma fa kafin zaben nasa idan ba a manta ba, ya wakilci shugaban majalisar ECOWAS Parliament din wajen jan ragamar wannan taro da a ka yi a Abujan.
Kuma sakamakon yadda su ‘yan majalisar ECOWAS din su ka amince da kaifin basirarsa da zalakarsa da hangen nesan sa da sanin yakamatansa tare da gogewarsa a irin wannan mu’amala a matakin kasa da na wannan nahiyar tamu ta Afirka, ya sa su ka ga dacewar zaben sa ya zama mataimakin wannan majalisa ta ECOWAS.
To tun daga nan fa likkafa take ta kara yin gaba ba kakkautawa. Shi fa wannan bawan Allah bai yarda da cewar wai iya hangensa iya mazabarsa ta Sanata ba. A’a, shi a wajen sa, jihar da kasar da nahiyar gaba daya, ya kamata a sa su a gaba dan samun ci gaban su. Shi ya sa ya amince cewar babban abinda zai tallafi rayuwar jama’a shine ya tallafawa rayuwar su ta karatu.
Fahimtar hakan ce ta sa ya dauki nauyin karatun dubunnan matasa dan karatun Digiri na daya da Digiri na biyu a manyan jami’o’in cikin gida Najeriya da ma na kasashen waje. Shi a kullum babban burinsa shine ilimi ilimi ilimi. Ya yarda ya kuma sakankance cewar ilimi shine babban mabudin gyaran rayuwa.
Kuma fa dan ya tabbatar maka da cewa shi fa ba dawurwura yake iya mazabarsa ba (wato local champion), wadanda suke cin gajiyar wannan shirin nasa na daukar nauyin karatun su ya faro daga mazabarsa ta Sanata, wato Kano Ta Arewa, zuwa jihar gaba daya.
Kuma fa hakan ba a ma yi maganar yadda yake tallafawa ragowar bangarorin ilimi na firamare da sakandare ba. Wanda a karkashin wadannan matakan akwai maganar giggina ajujuwa da bayar da kayan karatu na littattafai da kuma dinka kayan makaranta ga wadannan matakai na ilimi.
Wani abinda nake son a ma kara lura da shi shine, ko da fa a ce wannan Sanatan saboda dattako da yakana da girmama dan Adam, ya nuna cewar iyakacin ikonsa ya tsaya ne a mazabar sa ta Kano Ta Arewa, to tabbas kuma fa a kara fahimtar cewa, soyayyar da a ke masa ta karade jihar da Arewacin Najeriya da kuma wurare da yawan gaske.
Shi fa Sanata Barau baya ga cewar shi ba LOCAL CHAMPION ba ne, kuma ba dan siyasar da ya takaitu ga iyakacin karamar hukumar sa ba ne, shi dan majalisa ne da ya yarda cewar ya kamata a ce amfanin sa ya karade kasar gaba daya.
Ina rokon mai karantu da ya je ya bincika ire-iren kudurorin da ya gabatar a Majalisar Dattawa ya bi sawun su suka sami sahalewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dan ci gaban kasa gaba daya.
Ni fa na gamsu da cewar tarihin siyasar kasar nan ya na rubuta alherin da wannan Sanata ke shimfidawa kasar nan dan ci gaban siyasar kasar da dorewar mulkin dimukuradiyya. Tarihin siyasar kasar nan, zai kara cika cif-cif da ayyukan alherin da wannan bawan Allah ke haifarwa ga kasar tamu.
A halin da a ke ciki fa yanzu a jam’iyyar APC ta kasa ma gaba daya, Sanata Barau ya na daga cikin jiga-jiganta. Wannan ba wata sabuwar magana ba ce da take bukatar wata fassara ta daban. Abu ne wanda yake ga shi nan a fili baro-baro.
Matsalar dake damun wasu shine yadda suke yi masa kallon Barau a sunan sa na Barau kawai ba tare da sun kalle shi ta bangaren matsayin sa ba ko kallon yadda yake yin tasiri ga rayuwar al’ummar sa ba. Amma zancen gaskiya shine, sunan sa kawai ya na da wani tasiri na musamman a fagen siyasar kasar nan. Ni kullum fa ina yi masa kallon dattijon mutum kamilalle wanda ya san mutuncin kowa, kuma shugaba mara kwarafniya.
Gaskiya ne shi mutum ne wanda tun da can ma kafin ya zama mataimakin majalisar ECOWAS idonsa a bude yake kan abubuwan da ka je ka zo a bangaren siyasar kasa da ta nahiyar nan tamu ta Afirka.
Amma fa daga lokacin da a ka yi bikin bude babban taron majalisar ECOWAS na 2025 a jihar Lagos, ya kara samun tagomashi da karbuwa a siyasar Afirka ta Yamma.
A wannan taron ne fa ya kara nuna irin hobbasar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yake yi dan ci gaban kasar tare da samun hadin kan wannan nahiya tamu ta Afirka. Sanatan ya nuna hazaka da zalaka wajen kara tabbatar da cewa shi din fa akwai kaifin basirar gane alakar Najeriya da kasashen waje. Tare da fahimtar hanyoyin da a ke bukata dan samun cigaba mai ma’ana na wannan kasa.
An kara sanin wanene Sanata Barau a kasashen waje lokacin da ya halarci taron kasa da kasa na 18 na ‘yan majalisun kungiyar nan ta hadin kan kasashen Musulunci, wato Organization of Islamic Cooperation. Wanda a ka yi a garin
Abidjan, na kasar Cote d’Ivoire.
Yadda ya gabatar da makaloli da kuma yadda ya bayar da tasa gudunmawar wajen tattauna manyan abubuwan da a ka yi nazarinsu a taron. Ya sanya mamaki na gaske ga dukkanin mahalarta taron. Sai da kowa ya sara masa tare da kara jinjinawa kasar nan a dalilin yadda ya tattauna muhimman abubuwan da a ka tattauna a wajen.
Kwanan nan kuma ya halarci taron majalisun kasashen rainon Ingila na 68 a garin Barbados, wato Commonwealth Parliamentary Conference (CPC). A wajen taron kamar yadda ya saba a wasu sassa na tarurrukan duniya, Sanatan ya yi rawar gani. Kai da gani ka san ba dan koyo ba ne. Kuma ba kifin rijiya ba ne.
Ni fa a waje na duk wani da yake ganin kamar wannan bawan Allah karansa bai kai tsaiko ba, to zan iya cewa shi mai irin wannan tunanin idonsa a makance yake da son zuciya. Kuma tattare yake da cakuda al’amura ba tare da tunanin kifi na ganin ka mai jar koma ba.
Sanata Barau ya fara daga mazabar da yake wakilta, ya game da jihar Kano, ya karade wannan kasa sannan kuma ya dosano sassan duniya. Maganar kifin rijiya sai dai a tura ta can wani wajen ba kan Barau ba.
Anwar ya rubuto wannan daga Kano
Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025