Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada aniyarsa na ci gaba da ayyuka don amfanar al’ummar jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yau da ya karɓi shaidar samun nasarar zaɓen gwaji da Matashiya TV ta shirya tsakaninsa da Sanata Barau I Jibrin tsawon mako guda.
Gwamnan Alhaji Abba ya ce nasarar da ya samu za ta zamar masa ɗamba wajen cigaba da gudanar da ayyukan da ya ke yi musamman a bangaren ilimi, lafiya hanyoyi da sauransu.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin hadimunsa Alhaji Salisu Yahya Hotoro, ya ce sun yi matukar farin ciki da samun nasara a zaɓen.

Ya ce wannan ya nuna al’ummar jihar Kano su na tare da gwamnatin, da kuma amincewa da yadda ta ke gudanar da salon mulkinta.
Ya godewa Matashiya TV bisa shirya zaɓen wanda hakan zai ƙara ba su ƙwarin gwiwa da zaburar da su don ci gaba da gudanarwa da al’ummar Jihar ayyukan ci gaba.
A yayi jawabin shugaban Matashiya TV Alhaji Abubakar Murtala Ibrahim, ya bayyana cewa sun shirya taron ne, domin jin ra’ayin jama’a, don bayyana wanda su ke so ya zama gwamnan Kano a babban zaɓen 2027, tsakanin Sanata Barau da gwamna Abba.
A cewarsa ba ɗaukar nauyi a ka yi ba wajen shirya zaɓen, Matashiya TV ce ta ga dacewar ta shirya don ji daga al’ummar Jihar Kano, wanda su ke muradi ya zama gwamnan Jihar a zaɓen 2027.
Ya ƙara da cewa wannan ne karo na farko kuma Matashiya TV za ta ci gaba da shirya makamantan irin haka, tsakanin ƴan siyasa da kuma kamfanoni.
Shi ma ana shi jawabin manajan tashar Matashiya TV, kuma shugaban da ya jagoranci zaɓen, kuma ya sanar Dr Ashir Tukur Inuwa, ya ce an tsara zaɓen yadda ya kamata tare da bijiro da salo wanda ba a saba ganin haka ba.
Ya ce an shirya zaɓen da aka yi tsawon mako guda kuma a ka sanar a ranar Lahadi 12/10/2025.
An dai gudanar da zaben ne na tsawon mako guda wanda a ka fara daga ranar 4 ga watan Oktoban 2025, kuma a ka ƙare a ranar 11 ga watan, sannan a ka sanar da sakamakon a ranar Lahadi 12 ga watan na Oktoba.
Taron ya gudana ne a harabar Matashiya TV da ke a Kano a yau Talata, inda ya samu halartar wakilan gwamna, da sauran manyan baƙi.
