Ƙungiyar ma aikatan shari ar Najeriya reshen jihar Kaduna sun tafi yajin aikin sai baba ta gani da zai fara a gobe Litinin 27 ga watan Oktoba shekarar 2025, saboda gwamnatin jihar ta gaza biya musu bukatun su da su ka jima suna nema.

A wata sanarwa da a ka fitar bayan taron gaggawa da su ka yi, ƙungiyar ta ce ba ta da wani zaɓi da ya wuce su tafi yajin aikin sai baba ta gani.
Daga cikin abinda kungiyar ke bukata a samar musu da ƴancin gashin kansu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.

Sun buƙaci a ƙara musu albashi tare da biyan su albashin da a ka rike musu na watan Afrilu da Mayun shekarar 2021 da ragowar hakkokinsu su na shekara 9 da ya kai kaso 20 da ga shekarar 2016 zuwa yanzu, tallafin tafiye tafiye da kuma alawus din kayan sawar aikin ma aikatan.

Ƙungiyar ta karƙare da cewa za su fara yajin aikin cikin kankanin lokaci a gobe Litinin, kuma duka ma’aikatan za su tsayar da aiki cak.
Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren reshen jihar Kaduna Nasir Haroun, ya kuma umarci duka kotuna da ofisoshin su a fadin jihar da su tabbatar da sun bi umarnin ƙungiyar.
