Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang ya ce ba zai Iya barin jam iyyar PDP ya koma Jam iyyar APC ba duk da matsin lamba da ya ke samu don ganin ya koma ciin jam’iyyar.

Gwamnan ya bayyana haka ne tayin da ya ke magana a wani taro da a ka yi a babban ɗakin taro da ke gwamnatin jihar, Mufwang ya ce Allah ne kaɗai da waɗanda a ka zaɓa za su iya gane inda siyasar shi ta dosa.


Ya ce ya na shan matsin lamba don ganin an shawo kansa ya koma cikin jam’iyyar APC, amma kuma ya ce ba wanda zai sa shi ya sauya sheƙa daga jam’iyyarsa.
A satin da ya gabata shugabannin jam iyyar APC a jihar Plateau sun ƙaryata rahoton da ya ke yawo cewa gwamna Mufwang ya na shirin komawa jam iyyar su.
Tsohon maitaimakin sakataren jam iyyar na kasa Festus Fuanter ya ce ba sa buƙatar kowa ya koma jam iyyar su, kowa yayi abinda ya ke gaban sa.
A cewarsa, waɗanda ke yaɗa labarin sauya sheƙarsa da kuma musantawa alama ce ta tsoron da ke tattare a tare da su, a don haka babu wanis hiri da ya ke yi don ganin ya sauya sheƙa daga jam’iyyarsa.
Ya ce kaso 60 zuwa 70 na ƴan jam’iyyar APC a jihar Plateau za su yi murna da komawarsa, sai dai ya ce sun sani ba zai koma cikin jam’iyyar ba.
