Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa NEMA ta karbi ‘yan Najeriya 131 da suka dawo daga Agadez a Jamhuriyar Nijar, a karkashin shirin taimakawa ‘yan gudun hijira da hadin gwiwar gwamnatin tarayya ke tallafa wa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, hukumar ta ce wadanda suka dawo sun iso filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano a Alhamis 30 ga watan Oktoba.

NEMA ta ce jami’anta, tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure ta kasa, da masu ruwa da tsaki a harkar shige da fice a Najeriya, da sauran masu ruwa da tsaki ne suka tarbe su.

A cewar hukumar ta gudanar da rajista da kuma takardun shaida don tabbatar da tantancewa da kuma tallafawa yadda ya kamata.

Sanarwar ta kara da cewa daga baya an kai wadanda suka dawo zuwa makarantar horaswa ta hukumar shige da fice ta Najeriya a Kano.

NEMA ta ce daga cikin Mutane 131 da suka dawo, sun hada da manya maza 118, manya mata hudu, yara maza biyu, da yara mata bakwai.

Hukumar ta yi nuni da cewa a bisa kudirin gwamnatin tarayya na tabbatar da dawowar ‘yan Najeriya cikin aminci, mutunci da mutuntawa, an bai’wa wadanda suka dawo tallafin jin kai da suka hada da abinci, ruwan sha, duba lafiyar su, motocin daukar marasa lafiya, taimakon kayan aiki da kuma yi musu liyafa.

Ta kara da cewa hakan na nuna ci gaba da hadin gwiwa tsakanin NEMA, IOM, NCFRMI da sauran abokan hulda wajen tabbatar da ganin an dawo da ‘yan Najeriya, da suka dawo bisa radin kansu daga ketare, a matsayin wani bangare na kokarin kasa na ci gaba da inganta hijira cikin aminci da kuma karfafa tsarin tallafin jin kai.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: