‎Daga Abba Anwar, Kano

‎Ko da yake ina cikin jimamin rasuwar surukata, Hajiya Halima Mohammed Ibrahim Tsofo, wadda ta rasu yau kwana uku kenan a Maiduguri, na nemi da na yi wannan rubutun ne, duk da cewar a takaice ne, saboda muhimmancinsa da halin da ake ciki.

 

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin (CFR), ya ga dacewar yin tsokaci kan sabbin hafsoshin tsaron da aka nada. A cewarsa, wajibi ne su kasance masu cikakken goyon baya ga Shugaban Ƙasa da kuma Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

‎Sanata Barau, wanda aka fi sani da ɗan gwagwarmayar dimokuraɗiyya kuma mai kishin ƙasa, ya bayyana hakan ne yayin zaman Majalisar Dattawa na tantance sabbin hafsoshin tsaro da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR) ya gabatar domin tantancewa da amincewa a zauren majalisar dattawan kasa.

‎A cewar Barau, “Cikakken goyon baya ga Shugaban Ƙasa da ofishinsa da kuma Kundin Tsarin Mulki ne kadai zai bai wa ƙasarmu damar taka muhimmiyar rawa a cikin jerin ƙasashen da ke girmama doka da oda a duniya.”

‎Ya ƙara da cewa, kasancewar hafsoshin tsaro na da muhimmin alaƙa da shugaban ƙasa a tsarin mulkin Najeriya, to wajibi ne su kasance masu gaskiya da biyayya domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasa da wajen ta.

‎Yayin zaman majalisar na tantancewa da kuma bayan kammalawa, Sanata Barau ya kasance ɗaya daga cikin muryoyin da suka fi bayyana ƙwarai wajen jaddada muhimmancin aminci, biyayya da gaskiya ga gwamnati da tsarin mulkin ƙasa baki ɗaya.

‎A wani saƙonsa da ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan amincewa da sabbin hafsoshin tsaro, Sanata Barau ya rubuta cewa, “A yau a Majalisar Dattawa mun tantance kuma mun amince da waɗanda Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya gabatar domin su zama sabbin hafsoshin tsaro.”

‎Ya bayyana sunayen waɗanda aka amince da su, kamar haka, ” Laftanar Janar Olufemi Oluyede, Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar W. Shaibu, Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Rear Admiral I. Abbas, Babban Hafsan Rundunar Sojan Ruwa da Air Vice Marshal S.K. Aneke, Babban Hafsan Rundunar Sojan Sama.

Sanata Barau ya bayyana cewa tantancewar ta gudana cikin gaskiya da adalci, inda aka ba kowane ɗan majalisa damar tambayar sabbin hafsoshin tsaron tambayoyi a fili da kuma a zaman sirri.

‎Yayin da yake yabawa Shugaban Ƙasa Tinubu bisa zaben mutanen da ya kira “fitattun hafsoshi daga cikin mafi nagarta a rundunar tsaro,” Sanata Barau ya ce:

‎“Ina gode wa Shugaban Ƙasa saboda zaben kwararrun hafsoshi waɗanda za su tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya. Wannan alama ce ta shugabanci nagari da hangen nesa.”

‎A lokacin da yake magana kan ɗaya daga cikin sabbin hafsoshin tsaro – Babban Hafsan Rundunar Sojan Ruwa, Rear Admiral I. Abbas, wanda yake daga Jihar Kano, Sanata Barau ya nuna farin ciki bisa wannan zaben, yana mai cewa,

‎“Ina godiya ga Shugaban Ƙasa saboda zaben ɗan Kano mai jajircewa da kwarewa a harkar tsaro. Al’ummar Kano suna godiya ƙwarai da wannan karamci.”

‎A cewar wasu daga cikin mutanen Kano da na tattauna da na tattauna da su, sun bayyana gamsuwa da irin jajircewar Sanata Barau wajen kare muradun jihar da al’ummarta a matakin ƙasa.

 

Sa’annan kuma jama’ar Kano din sun yabawa Sanata Barau ganin irin rawar da ya taka wajen ganin ba a bar Kano a baya ba a irin wadannan nade-naden mukaman. An fahimci rawar da ya taka wajen ganin Kano ba a bar ta a baya ba. Wani ya ce, “Barau bawan Allah.”

‎Sanata Barau, wanda ya dade yana fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya mai inganci da tsari a Najeriya, ya ƙara jaddada amincinsa ga shugabancin Shugaban Ƙasa Tinubu, yana mai cewa, “Ina da tabbacin cewa tare da waɗannan sabbin hafsoshin tsaro, burin Shugaban Ƙasa na samar da cikakken tsaro a Najeriya zai tabbata, Insha Allah.”

‎A karshe, Sanata Barau ya ja hankalin sabbin hafsoshin tsaron da su tsaya tsayin daka wajen kare martabar Kundin Tsarin Mulki da kuma nuna cikakkiyar biyayya ga Shugaban Ƙasa da al’ummar Najeriya baki ɗaya.

‎Anwar ya rubuta daga Kano,

‎Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025.

Leave a Reply

%d bloggers like this: