Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta ce wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Alhaji Muhammad Sama’ila-Bagudo a karamar hukumar Bagudo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nafi’u Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Birnin Kebbi.

A cewar Kakakin an yi garkuwa da shi ne a daren Juma’a da misalin karfe 8:20 na dare, inda wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin Bagudo, suka kama dan majalisar jim kadan bayan ya idar da sallar isha’i a hanyarsa ta komawa gida.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kara da cewa, rundunar ta gaggauta tura tawagar hadin gwiwa da suka hada da jami’an tsaro na ‘yan sanda, jami’an soji, da kuma ‘yan banga na yankin domin bin sahun wadanda suka yi garkuwa da shi, tare da tabbatar da ceto mataimakin shugaban majalisar.

A halin yanzu dai rundunar hadin guiwa na bin hanyar da ‘yan bindigar ke bi da kuma dazuzzukan da ke kusa da su da nufin ceto dan majalisar ba tare da wani rauni ba, tare kuma da kama wadanda suka yi garkuwa da shi ɗin.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda a jihar Bello Sani ya jaddada aniyar rundunar na kare rayuka da dukiyoyin mazauna fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: