Rundunar sojin Najeriya ta ce jami’anta sun zafafa kai hare-hare kan ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a fadin kasar, inda suka ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su, tare da kama mutane 20 da ake zargi, tare da kashe ‘yan ta’adda biyu cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Asabar din nan, ta ce an gudanar da ayyukan hadin gwiwa a yankunan Arewa maso gabas, Arewa maso yamma, Arewa ta Tsakiya, da kuma Kudu maso Kudu.

Sanarwar ta ce A Arewa maso gabas, jami’an bataliya ta 192, tare da hadin gwiwar jami’an hadin gwiwa na farar hula, suka yi musayar wuta da da ƴan ta’addan a kauyen Hudugum da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, inda suka yi nasarar tarwatsa kungiyoyin ‘yan ta’addan biyu a wani samame da suka yi.

Rundunar ta kara da cewa wasu shugabannin ‘yan ta’adda Fannami Ari wanda aka fi sani da Abu Dujana, Hussaini Hassan Modu da aka fi sani Abu Yusuf, da kuma wani wanda ake horas da su sun mika wuya ga sojoji a kananan hukumomin Kukawa da Damboa.

Sanarwar ta bayyana cewa a yankin Arewa maso yamma, sojojin runduna ta daya sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane biyu a jihar Zamfara, inda suka kubtar da wasu mutane 11 da aka yi garkuwa da su a wani samame daban-daban a kan hanyar Magami-Jan Gemi da Kucheri-Bilbis, inda aka sada wadanda aka ceto ga iyalansu.

Yayin da sojoji ke ci gaba da sintiri na yaki da ta’addanci don hana ‘yan ta’adda ƴancin yin walwala da kuma dakile hanyoyin da suke amfani da su.

A shiyyar Arewa ta tsakiya kuwa hadakar jami’an sun kai samame na hadin gwiwa a fadin jihohin Filato, Benue, Nasarawa da Kaduna, inda aka kama wasu mutane 15 da ake zargi da alaka da kungiyoyin asiri, garkuwa da mutane, satar shanu, da rikicin kabilanci, An kuma ceto mutane hudu da aka yi garkuwa da su a yayin sumamen.

Hakazalika sanarwar ta ce sojoji a yankin Kudu-maso-Kudu sun gano tare da tarwatsa wasu sansanonin tace man fetur ba bisa ka’ida ba, a Biseni da ke karamar hukumar Yenagoa ta jihar Bayelsa, tare da kama jarka 62 na danyen mai da aka sace, wanda aka kiyasta sama da lita 3,000 a karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo.

Rundunar sojin ta ce ta na ci gaba da jajircewa wajen kawo ƙarshen dukkan wani makiyin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: