Jami’an rundunar ‘yan sanda na Operation Doo Akpor a jihar Bayelsa, sun kama wani sufeton ‘yan sanda mai suna Sunday Idey bisa zarginsa da cin zarafin ‘ya’yansa uku bisa zarginsu da maita da shiga kungiyar asiri.

jami’in wanda ke aiki a sashin yaki da cin hanci da rashawa na sashin ‘yan sandan Igbogene, an kama shi da cin zarafin ‘ya’yan nasa ne a karshen mako bisa zargin cewa su da shiga kungiyar asiri.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Francis Idu, ya ce an kama jami’in, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike akansa lamarin.

A cewar shaidun gani da ido, makwabtan jami’in ne suka yi gaggawar sanar da jami’an ƴan sandan kan cin zarafin da mahaifinnasu ke yi musu, inda da zuwansu suka kai yaran asibiti domin yi musu magani.

A halin yanzu dai ana ci gaba da bincike akan wanda ake zargin, kafin daukar mataki.
