Gwamnan Jihar Ebonyi Francis Nwifuru ya taya gwamnan Jihar Anambra Chukwuma Soludo murnar sake zabensa a matsayin gwamnan jihar Anambra.

Nwifuru ya bayyana nasarar da Soludo ya samu a matsayin sa ke tabbatar da amincewar jama’a kan shugabancinsa da nasarorin da ya samu a cikin gwamnatinsa.

A wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa Monday Uzor ne ya fitar a ranar Lahadi, gwamnan ya ce sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 8 ga watan Nuwamba, ya nuna karara wajen nuna kyakykyawan ayyukan Soludo a wa’adinsa na farko.

Gwamna Nwifuru ya bayyana kwarin gwiwar cewa sake zaben Soludo zai kara karfafa manufofin dimokuradiyya, da inganta shugabanci na gari, da kuma karfafa sabunta ci gaban kabilar Igbo da ke da nufin daukaka yankin Kudu maso Gabas.

Gwamnan ya kuma nemi kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin jihohin Anambra da Ebonyi a kokarinsu na hadakar yankin, da sauye-sauyen tattalin arziki, da kuma ci gaban al’ummarsu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: