Gwamnatin jihar Zamfara ta raba magunguna cutar kwalara da nufin dakile yaduwar cutar a fadin kananan hukumomi 14 na jihar.

Kwamishiniyar lafiya a Jihar Dr Nafisa Muhammad Maradun ce ta kaddamar da rabon kayayyakin a Samaru da ke Gusau.
Ta ce rabon kayayyakin ya nuna yadda gwamnatin jihar ta yi gaggawar daukar matakan dakile barkewar cutar kwalara, inda ta jaddada cewa an bayar da dukkan kayayyakin kyauta tare da gargadin jami’an kiwon lafiya kan kin bai’wa majinyatan ko kuma karbar kudaden.

Dr Nafisa ta yi gargadin cewa dukkan wanda aka kama yana sayar da magungunan zai fuskanci fushin doka.

Ta kuma bukaci ma’aikatan lafiya da su kasance masu gaskiya da rikon amana, sannan kuma ta yi kira ga al’umma da su kai rahoton duk wani rashin da’a da aka gani da ya shafi amfani da su ko kuma karkatar da kayayyakin.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Magunguna ta Jihar Zamfara Sani Bello, ya bayyana matukar godiya ga gwamnan Jihar.
Hon Bello Jabaka shugaban karamar hukumar Maru, ya yabawa kwamishinar lafiya bisa jajircewar ta, ya kuma yaba da yadda gwamna Lawal ke ci gaba da tallafawa mazauna jihar.
