Gwamnan jihar Ogun Prince Dapo Abiodun ya taya takwaransa na Jihar Anambra Charles Soludo murnar sake zabensa.

A wata sanarwa da mai bai’wa gwamnan na Ogun shawara na musamman kan harkokin yada labarai Hon Kayode Akinmade ya fitar ya ce sakamakon zaben ya nuna a fili irin kwarin gwiwar da mutanen Anambra suke da shi kan shugabancin Soludo.
Soludo da ke cikin jam’iyyar APGA ya samu nasarar ne bisa samun kuri’u 422,664, inda ya kayar da sauran abokan takarar na jam’iyyar ADC, PDP da kuma APC.

Abiodun wanda shi ne Shugaban kungiyar gwamnonin yankin Kudu, inda ya bukace shi da ya ci gaba da tafiyar da manufofinsa da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa.

Ya kuma kara da karfafawa Soludo gwiwa da ya hada kan muradun siyasa a fadin jihar domin samun ci gaba.
Gwamnan ya kuma yabawa Soludo bisa yadda yake kulla kyakkyawar alaka ta aiki da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya bukace shi da ya ci gaba da bin tsarin dimokuradiyya da shugabanci na gari.
