Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya Chukwuma Soludo gwamnan Jihar Anambra murnar sake lashe zabensa da aka yi a matsayin gwamnan jihar.

A cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa shugaba Tinubu ya bayyana sake zaben Soludo a matsayin wata shaida da ke nuna hangen nesan shugabancinsa da kuma gagarumin ci gaban da aka samu a gwamnatinsa.
Shugaban ya ce gwamna Soludo ya kasance gwamna mai jajircewa a cikin ayyukansu, inda ya ce ko da a watan Mayun 2025, inda ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatinsa ta aiwatar, wanda hakan ya nuna kwarewarsa a cikin harkokin ci gaban al’umma.

Shugaban ya kuma yaba masa bisa yadda ya kawo da’a, alheri, hazaka, da kuma sabon salon mulki a Anambra a karkashinsa.

Shugaba Tinubu ya kuma tabbatar da goyon bayansa ga gwamna Soludo, tare da fatan ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin Anambra da gwamnatin Tarayya.
Shugaba Tinubu ya kuma yabawa sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Ƙasa INEC Joash Amupitan da jami’ansa, bisa gudanar da abin da ya bayyana a matsayin sahihin zabe, bisa rahotannin da aka samu kawo yanzu.
Ya kuma umarci hukumar da ta ci gaba da tsare-tsarenta da kuma ci gaba da inganta ayyukanta domin ƙara karfafa tsarin zaben.
An dai gudanar da zaben ne a ranar Asabar, inda kuma aka sanar da sakamakon zaben a yau Lahadi.
