Wasu ƴan bindiga sun hallaka wata mata mai juna biyu da wasu mutane hudu a wani hari da suka kai kauyen Alkalije da ke karamar hukumar Yabo a jihar Sokoto.

Rahotanni sun ce maharan sun mamaye mutane garin ne da sanyin safiyar ranar Litinin, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Kauyen Alkalije da ke karkashin yankin Kilgori na da iyaka da karamar hukumar Silame da wasu yankuna a jihar Kebbi.

A cewar majiyoyin yankin, wasu mutanen biyu sun samu raunuka a harbin bindiga kuma suna karbar magani a wani asibiti da ke kusa.

Wani shugaban al’ummar da ya nemi a sakaya sunansa, ya koka kan yadda wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton suna tsallakawa Jihar ne daga jihar Kebbi ke kai wa kauyukansu su kai musu hari, tare da sace mutane.

Shugaban al’ummar ya roki gwamnati da ta samar da sansanin tsaro a yankin domin taimakawa wajen dakile hare-haren, yana mai cewa a halin yanzu babu.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar DSP Ahmad Rufa’i, ya ce har yanzu bai samu rahoton faruwar lamarin ba, inda ya bayyana cewa zai yi bincike.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: