Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta bayar da umarnin haramta samarwa da sayar da barasa a cikin buhuna da kwalabe da bai wuce milliliters 200 ba nan da watan Disamba 2025.

Shugabar hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayar da umarnin, a lokacin da ta ke ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja a ranar Talata.

Shugabar ta bayyana cewa matakin na daya daga cikin kokarin da ake na magance matsalar shan barasa mai arha a tsakanin matasa da direbobi.

Kazalika ta kara da cewa haka na barazana ga laiyar al’umma da yawaitar tashe-tashen hankula a cikin gida, hadurra akan titina, munanan halaye a tsakanin al’umma, da dai sauransu.

A cewar ta, umarnin ya biyo bayan wani kuduri da majalisar dattawan ta yi na nuna damuwa game da yawaitar barasa da ke kunshe a cikin kwalabe da kananan yara ke sha hakan na hadda matasalolin zamantakewa.

Adeyeye ta bayyana cewa tun da farko hukumar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tare da masu ruwa da tsaki a masana’antu don tsagaita wa, inda a baya aka sanya wa’adin daga shekarar 2023 zuwa Disamba 2025.

Adeyeye ta ce haramcin ba hukunci bane, amma kariya ne don kare lafiya da walwalar ‘yan Najeriya.
Ta kuma bayyana cewa hukumar za ta hada kai da jami’an tsaro domin tabbatar da aiwatar da dokar da aka shirya farawa a watan Janairun 2026.

Leave a Reply

%d bloggers like this: