Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a karo na biyu ta haramta wa jam’iyyar PDP gudanar da babban taronta na kasa da ta shirya gudanarwa a garin Ibadan na jihar Oyo tsakanin ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.

Kotun ta kuma haramtawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC sa ido,ko kuma sanin sakamakon zaben, inda ake sa ran za a zabi shugaban jam’iyyar na da shugaban kasa.

Alkalin kotun mai shari’a Peter Lifu ne ya bayar da sabon umarnin a ranar Talata a lokacin da yake yanke hukunci a cikin takardar bukatar da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya gabatar.

Lamido dai ya kai jam’iyyar kara gaban kotun, inda ya yi korafin cewa an hana shi sayen fom din tsayawa takarar shugaban kasa domin samun damar halartar taron.

Ya ce jam’iyyar ta gaza bin sharuddan da dokokin da suka dace don gudanar da irin wadannan tarurrukan.

Alkalin kotun ya ce shaidun da Lamido ya bayar sun nuna cewa ba samar da jadawalin taron ba mambobinsa kamar yadda doka ta tanada.
A cewar mai shari’a, a kundin tsarin mulkin kasar, dole ne masu rike da madafun iko su bi ka’idojin da suka dace, inda ya kara da cewa yin hakan ba zai haifar da barazana ga dimokuradiyyar kanta ba.
Ya kuma ce bisa ga sashe na 6 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999, bai kamata kotun shari’a ta yi watsi da rawar da take takawa ba na tabbatar da adalci ba tare da tsoro ko kuma nuna son kai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: