Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kasar za ta shawo kan matsalar rashin tsaro da sauran matsalolin da ke addabar ta, yayin da ya bukaci ‘yan kasar da su karfafa hadin kai da kuma yin aiki tare domin ci gaban kasa.

Ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a wajen taron bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a dakin taro na Arewa House da ke Kaduna.

Sanwo-Olu ya ce za su kawo karshen talauci, yunwa, kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tunatar da su a farkon wannan makon.

Ya yi tsokaci na musamman kan ikirarin da Amurka ta yi a baya-bayan nan game da kisan kare dangi kan kiristoci a Najeriya, inda ya jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin ‘yan kasa na addinai daban-daban.

Acewarsa za su ci gaba da tabbatar da cewa Najeriya kasa ce mai alfahari da kabilanci da addini da kuma al’adu daban-daban.

Gwamnan ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi tsarin mulki na gida da kasa, musamman wajen magance matsalar rashin tsaro.

Sanwo-Olu ya kuma nanata rawar da gwamnatin Tarayya ke tawa ta hanyar sabunta fata na magance tsaro da ci gaban kasa.

Ya ce shirin da Tinubu ke jagoranta an tsara shi ne don tabbatar da habakar tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, inganta jarin ƴan kasa, da sake fasalin harkokin mulki baki daya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: