Jam’iyyar PDP reshen jihar Sokoto ta kaddamar da wani kwamiti da zai tsara yadda jihar za ta halarci babban taron jam’iyyar na kasa da za a fudanar a watan Nuwamban nan.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a yau Talata a wani taro da ta gudanar a Sokoto bisa jagorancin shugaban jam’iyyar na Jihar Muhammadu Goronyo, inda ya gargadi mambobin jam’iyyar da su kiyaye martabar hadin kai, da’a, da biyayya ga jam’iyyar.
Goronyo ya bukaci kwamitin da ya kare, tare da ciyar da muradun jam’iyyar gaba a yayin babban taron na kasa da aka shirya gudanarwa a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, yana mai jaddada cewa dole ne jam’iyyar PDP ta Sokoto ta yi koyi da tsarin dimokuradiyya na cikin gida da kuma nagartattun jam’iyyu.

A cewar wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar Hassan Sanyinnawal ya fitar, ya ce kwamitin na karkashin jagorancin sakataren tsare-tsaren jam’iyyar Abubakar Shuni, yayin da mataimakin sakataren Mustapha Gidadawa zai kasance a matsayin sakatare.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Abubakar Magaji, da Abdullahi Yabo, Abdulrahaman Abubakar mai ba da shawara kan harkokin shari’a na jihar, Nasiru Kware, Hassan Sanyinnawal sakataren yada labarai, Bello Mai Karfi shagaban jam’iyyar na kananan hukumomi, da kuma Atiku Yabo shugaban matasan shiyyar Arewa maso Yamma jam’iyyar.
Sanyinnawal ya ce aikin kwamitin shi ne tabbatar da gudanar da sahihin aiki tare da halartar wakilan Sokoto a wajen taron na kasa, yana mai bayyana kaddamar da taron a matsayin tsayawa tsayin daka na jam’iyyar wajen tabbatar da dimokuradiyyar cikin gida da kuma zaben shugabanni masu inganci.
Ya kuma yi kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar da su marawa kwamitin baya domin ganin an samun nasara wanda zai kara karfafa jam’iyyar PDP gabanin zabe mai zuwa.
Hakan dai na zuwa ne bayan umarnin kotun tarayya a Abuja a yau Talata, na haramtawa jam’iyyar gudanar da taronta na ƙasa da ta ke shirin gudanarwa a watan Nuwamban nan.
