Tsohon gwamnan jihar Abia kuma sanata mai ci a yanzu Sanata Orji Uzor Kalu, ya yi imanin cewa babu wadda zai fuskantar shugaban ƙasa Bola Tinubu a yayin zaben shugaban kasa a 2027 a matsayin yin takara da shi, inda ya bayyana cewa takara za ta kasance ne ta Tinubu kawai.

Sanata Kalu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da mambobin kungiyar ‘yan jarida ta majalisar dattawa a zauren majalisar a ranar Talata.
Sanata Kalu wanda shine shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da hukumar raya kudu maso gabas, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta tsaya tsayin daka a fadin kasar nan kuma tana ci gaba da samun gagarumin goyon baya tun daga tushe.

Acewarsa babu wani wanda zai iya yin takara da shugaba Tinubu, yana mai cewa za su ci gaba da yin duk abinda ya kamata domin taimakawa ƴan Najeriya wajen ci gabansu.

Har ila yau ya ce majalisar dattawa karkashin shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio, ta mayar da hankali ne wajen zartar da dokokin da za su taimaka wa yunkurin farfado da tattalin arzikin shugaban kasar.
Da yake mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan zargin yiwa kiristoci kisan kare dangi a Najeriya, Kalu ya ce aikata ta’addanci da ake yi a Najeriya ya shafi musulmai da kiristoci ne.
