Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe dukkan kanana da manyan makaratu a faɗin jihar da su ka haɗa da kwalegojijn ilimi da kuma jami’oi nan take.

Hakan ba ya rasa nasaba da matsalar rashin tsaro da yai ƙamari a ƙasar da kuma yawan hare haren da Boko haram ke kaiwa jami’an tsaro da kuma fararen hula tare da kwashe ɗalibai a jihar Niger da kuma Kebbi ya sanya daukar wannan matakin.


Kwamishinan ƴan sanda na jihar Bauchi ya tabbatar da kashe wasu jami’ansu biyar a ranar Lahadi da yan ta’adda su ka yi a kauyen Sabon Sara da ke karamar hukumar Darazo a jihar.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Ilimi ta jihar Jalahudden Usman ya sanyawa hannu, ya ce rufe makarantun ya biyo bayan wata muhimmiyar ganawa da su ka yi a kan yadda za’a kare dalibai da kuma malaman a fadin jihar baki ɗaya.
Sanarwa ta kuma ƙara da cewa rufe makarantun ba abu bane mai daɗi sai don tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiya ga malamai da daliban .
Kare dukkan wani dalibi dake jihar Bauchi hakki ne da ya rataya a kansu tare da tabbatar da bayar da tsaro wajan koyo da koyarwa cikin Aminci ba tare da fargaba ko tsaro ba a cewar sanarwar.
Gwamnatin ta yi kira ga iyaye da kuma wakilan al’umma da su tabbatar da bayar da haɗin kai ga matakin gwamnati.
Sanarwar ta ce gwamnati na cigaba da ƙoƙarin ta tare da aiki da jami’an tsaro don tabbatar da tsaro ta kuma bada ingantattan ilimi, kuma za a sanar da lokacin komawa makarantun idan komai ya dai dai ta.
Sanarwa ta kuma ƙara jaddada aniyar gwamnati na cigaba da samar da sabbin abubuwa da za su taimakawa jihar baki daya.
