Tsohon ministan shari’a a Najeriya Abubakar Malami ya musanta zargin ɗaukar nauyin ƴan ta’adda bayan wallafa sunansa a cikin waɗanda ke taimaka musu.

Malami ta bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa jiya Juma’a wanda ya ce zargin ba shi da tushe balle makama.

A cewarsa ba a taɓa tuhumarsa ko bincikensa ko zarginsa daga kowacce hukuma ba a Najeriya da wajen Najeriya kan makamancin wannan zargi.

Ya ƙara da cewa jami’in soja mai ritaya da ya yi magana bai bayyana shi a matsayin wanda a ke zargi ko wani a kan ta’addanci ba.

Ya ƙara da cewa zargin hannu a ta’addanci babban lamari ne kuma duk wanda zai yi shi sai ya kawo kwararan hujjoji a kai.

Malami ya bayyana yadda ya ke mutunta yan jarida da kafofin yaɗa labarai inda ya buƙaci masu wallafa labarai da su dinga bibiya da tabbatarwa kafin wallafa komai a kai.

Domin a cewarsa irin haka da sunan bata suna na iya kawo al’umma su daina yarda da da ɓangaren kuma na iya shafar tsaron ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: