Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya ce har yanzu shi mamba ne a jam’iyyar PDP.

Wike ya bayyana haka ne yayin da ya ke mayar da jawabi a jiya Juma’a dangane da sauya shekar da wasu ƴan majalisa 16 su ka yi zuwa jam’iyya APC.

Ƴan majalisar da kakakinsu sun sanar da sauya shekar ne a jiya Juma’a bayan wani zaman tattaunawa da su ka yi.

Da ya ke yi wa manema labarai bayani jiya jim kaɗan bayan sanar da sauya shekar, Wike ya ce ƴan majalisar da su ka sauya sheka ba su tuntubeshi ba sun yanke shawarar ne bisa ra’ayi da ƴancin kansu.

Wike ya bayyana haka yayin duba wasu ayyukan tituna da ya ke jagoranta a Abuja.

Ya ce duk da cewar wasu daga cikin yan majalisar 16 ne su ka sauya shekar, amma har yanzu akwai wasu guda 10 da su ke cikin jam’iyyar PDP kuma za su ci gaba da aiki tare.

Yayin da a ka tambayeshi kan zargin ko da sa hannunsa ta ƙarƙashin ƙasa su ka koma, ya ce wannan abin takaici ne domin kowanne mutum ya na da ra’ayi na zabin abinda ya ke so.

A cewarsa, duk da sauya shekar da ƴan majalisar su ka yi za su ci gaba da aiki tare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: