Gwamitin tantancewa na jam’iyyar Accord Party sun tabbatar da governor Ademola Adeleke a matsayin dan takarar fidda gwani da aka gudanar ranar Laraba a Osogbo.

Hakan na cikin sanarwa da shuagaban kwamitin tantancewa ya fitar ta hannun sakataran jam’iyyar Ibe Thankgod.
Thankgod yace Adeleke ya cika dukkan sharudan zama dan takara fidda gwani ,kuma shi kadai ne yasai tikiti ,wanda hakan ya bashi damar zama cikakken dan takarar a jam’iyyar .

Ya kuma bayyana shi a matsayin wanda ya cancanta bisa takarar daya tsaya .

Cikin jawabin da Adeleke yayi ya godewa yan kwamitin tantancewa da shugabanin jam’iyya, inda yace a shirye yake daya jagoranci jam’iyyar Accord Party tare da yin nasara a shekarar 2026.
Inda yace a shirya yake tsaf wajen yin zaɓen fidda gwani da kuma babban zaɓe.
Kazalika ya kuma kara da cewa zasuyi nasara da ikon Allah.
Adeleke ya bayyana komawarsa zuwa jam’iyyar Accord Party a daren jiya Talata bayan yayi murabus daga jam’iyyar PDP a ranar 2 ga watan Disamba.
