Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi barazanar soke izinin yin amfani da filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal, babban birnin jihar, wanda ya ba dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar domin gangamin kamfen.

Gwamnan ya ce sama da wata daya ke nan babban daraktan yakin neman zaben Atiku a jihar, Dokta Abiye Sekibo, na sintiri a filin gabanin taron da za su gudanar ranar 11 ga watan Fabrairu mai zuwa.
Wike ya ce sun ba da filin domin gudanar da taron ba tare da an biya su ko sisi ba, inda ya ce za a damka musu shi ana saura kwana biyu kafin ranar taron.

Sai dai yayin gangamin yakin neman zaben PDP a Karamar Hukumar Oyigbo da ke Jihar ranar Juma’a, Gwamnan ya ce Abiye ba shi da hurumin da zai karbe wajen tun ana saura wata daya kafin ranar taron nasu.

kuma gwamnan ya ja kunnen dan siyasar da kada ya fusata su ta hanyar yunkurin karbe filin, wanda mallakin Gwamnatin Jihar ne tun ana makonni kafin ranar, in ba haka ba kuma su soke izinin.