Tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasa a Jami’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya ce, waɗanda suke tunanin zai bar Najeriya bayan zaɓe su ma daina wannan tunanin.

Yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai da ya kira, a yau Litinin a birnin tarayya Abuja.
Atiku ya ce “babu inda zan je, matsawar ina numfashi zan ci gaba da fafutuka tare da sauran ƴan Najeriya, dan tabbatar da dimukuraɗiyya da doka dan kyautatuwar siyasa da bunƙasa tattalin arziƙi dole ƙasa na buƙatar kai wa babban bigire.”

“gwagwarmayar yanzu kuma tana buƙatar jagorancin matasan Najeriya, waɗanda su ke da fikira fiye da ta lokacinmu.”

Atiku kuma ya ce, dole dimukuraɗiyya ta kasance wani abu mai muhimmanci, kuma dole a wassafa ta cikin yanayin zaɓen gaskiya da gaskiya na adalci don girmama ra’ayin al’umma.
Atiku yace “dole mu tabbatar da yin zaɓe ta hanyar na’urar zamani, wannan ƙarni na 21 ne kuma ƙasashen da basu kai Najeriya cigaba ba ma sun rungumi tsarin, al’umma tana samun cigaba ne in ta karɓi sabbin tsarurruka.”
“kuma dole mu samar da cewa duk wasu ƙa’idoji dangane da taƙaddama yayin zaɓe dole a gama ta kafin a bayyana wanda yayi nasara”
Atiku ya ce “yanayin da ake yi yanzu tsakanin zaɓe da rantsar da wanda yayi nasara, bai kamata ace ya yi daidai da ƙa’idar zaɓe ba.”
A ƙarshe yayi kira da cewa, don a samar da haɗin kai da daidaito ga ƴan ƙasa, ya kamata a koma yin tsarin falle ɗaya na shekaru shida ga wa’adin mulkin shugaban ƙasa, don a dinga jujjuyawa zuwa kowacce shiyya.