DAGA RABIU SANUSI KATSINA.

Kisan wani Mutum mai shekaru 45 a jihar katsina ya tada hankalin mazauna anguwar yammawa.

Lamarin ya faru ne a makon daya gabata ne inda al’ummar unguwar yammawa suka tsinci kan su cikin tashin hankali sakamakon kisan wa ni mutum mai suna Alh, Abdullahi lawal da aka fi sani da Alili, wanda wa su da ba’asan kosuwa nene ba suka shiga gidan shi da ke yammawa cikin birnin katsina da misalin karfe 9:00 na dare.

Wnada suke makwabtaka da Alili sun tabbatar wa da wakilin mujallar matashiya cewa kafin rasuwar marigayin matukin motar daukar mai ne, wato tanka.
Haka zalika sun bayyana cewa mutumin a daren da abin yafaru sai da yayi wa dukkan abokanshi bankwana da suke tare daga bisani ya wuce zuwa gidan shi.
Shigar shi gida keda wahala yaran shi sukayi ma shi tarba cikin murna da annashuwa, bayan dan wa ni lokaci ya ce ma matanshi guda biyu ya gaji yana bukatar ya huta, nan ta ke yayi ma su bankwana ya wuce zuwa dakin sa.
Abin da bai sa ni ba ashe bankwana karshe yayi da iyalin na shi,inda cikin dan kankanin lokaci aka sameshi kwance cikin jini.

Wa ni makusancin mamacin ya tabbatar mana da cewa misalin karfe tara na dare makasan suka iske shi har dakin shi yayin da sukayi mashi harbi biyu ga kai da bindiga.
“Na farko dai sun tambayi kudi da wayoyi tare da tambayar ina Alili yake, suka duba cikin gidan daga bisani suka isa dakin shi, yayin da suka fito da shi daga cikin dakin suka kuma harbeshi a kai har sau biyu sukai fice abinsu batare da sun dauki komi ba” inji makwabtan shi.
Daga bisani an samu marigayi Abdullahi kwance cikin jini da harbi biyu daya a goshi sai daya a tsakiyar kan shi, anyi saurin kaishi asibiti amma a na isa aka tabbatar da ya rigamu gidan gaskiya.

Marigayin ya ra su dai yana da mata biyu Hadiza da Jamila sai yara 19 an mai sutura kamar yadda addini ya tanadar a ranar talata da safe.

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar Yan sandan jihar katsina ASP Anas Gezawa ya bayyana cewa ana cigaba da bincike dan gano Wanda sukayi kisan ko kuma suke da hannu a kisan.
Rundunar Yan sandar jihar Katsina tana kokari don ganin ta gano wayanda sukayi kisan tare da gurfanar dasu a gaban kuliya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: