Sanata Abdulaziz Yar’adua ya ce gwamnatin tarayya na shirin sake ɗaukar sabbin jami’an tsaro don daƙile yawan hare-hare da ke ƙaruwa a Najeriya.

Yar’adua ya bayyana haka ne yau Juma’a a yayin tattaunawa da gidan talabiji na Channels.
Ya ce shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na yin duk mai yuwuwa don ganin an samar da zaman lafiya tare da daƙile ayyukan ta’addanci a ƙasar.

Yar’adua wanda shi ne shugaban kwamitin sojoji a zauren majalisar dattawa, ya ce akwai ƙarancin jami’an tsaro a ƙasar wanda hakan ya sa ake samun ƙaruwar ayyukan ta’addanci.

A cewarsa, a wata ƙididiiga da aka fitar ta nuna cewar, a arewa maso yammacin Najeriya akwai ƴan bindiga sama da dubu talatin, 30,000 wanda ya ce dukkanin jami’an tsaro da ake da su a ƙasar ba su fi miliyan guda ba a ƙasar da ke da mutane sama da miliyan 200.
Ya ce la’akari da haka ya sa su ka gano ba za su iya magance matsalar tsaro ba har sai an yi gyara a ɓangaren.
