Kungiyar dattawan Arewa NEF ta nuna goyon bayanta ga malamin addinin musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Gumi kan yin sulhu da ‘yan ta’adda a Kasar.

Shugaban kungiyar Abdul-Aziz Sulaiman ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a yau Asabar.


Shugaban ya ce kungiyarsu na neman shugaba Tinubu ya bai’wa Sheikh Gumi damar tattaunawa da ‘yan bindiga a Kasar domin ceto daliban makarantar da aka yi garkuwa da su da sauran mutanen da ke hannunsu.
Shugaban ya kara da cewa yin sulhu da ‘yan bindiga ba ya na nufin kara musu kaimi ba ne a ayyukansu, sai don kawo karshen matsalar tsaro a Kasar.
Kungiyar ta bayyana cewa sulhun nada muhimmanci kuma hakan zai samar da mafita ga Kasar.
Kiran na kungiyar na zuwa ne bayan da Malam Gumi ya bukaci da gwamnatin tarayya ta bashi damar yin sulhu da ‘yan bindiga a kasar domin kawo karshen ta’addansu a dukkan fadin Kasar.
