Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada Zubaida Umar a matsayin shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa NEMA.

 

Mai magana da yawun shugaban kan yada Labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

 

Ajuri ya ce nadin shugabar hukumar zai fara aikin ne nan take.

 

Sanarwar ta ce shugaban ya kuma bukaci Zubaida ta yi aiki yadda ya kamata fiye da yadda ta yi aiki a ma’aikatun baya.

 

Kafin nadin Zubaida Umar ta shafe sama da shekaru 20 ta na gudanar da ayyuka a bangarori daban-daban na Kasar.

 

Zubaida ta yi aikin kula da Ma’aikatar harkokin kudi da gudanarwa, sannan ta na daya daga cikin ‘yan cibiyar kwararrun ma’aikatan banki da cibiyar bayar da lamuni da dai sauransu, a ma’aikatu daban-daban na Kasar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: