Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun kai hari garin Tsafe da ke cikin karamar hukumar ta Tsafe a Jihar Zamfara.

 

Jaridar Leadership ta rawaito cewa maharan sun hallaka wasu jami’an tsaron sa-kai, tare da kone wasu motocin sojoji guda biyu.

 

Wani mazaunin garin mai suna Malam Usman Tsafe ya shaidawa manema labarai cewa, yan ta’addan sun zagaye garin ne dauke da makamai.

 

Malam Usman ya ce bayan zuwan maharan sun raba kansu gida uku, inda kashi daya suka yi yunkurin kai hari kan Kwalejin horas da malaman lafiya da fasaha da ke garin na Tsafe.

 

Yayin da kashi biyun kuma suka kutsa cikin garin tare da bude wuta a cikin garin da niyar yin garkuwa da mutanen garin da kuma Daliban makaranta.

 

Tsafe ya kara da cewa taimakon gaggawa da jami’an tsaro suka kai garin ne ya tilastawa maharan tserewa daga garin.

 

Malam Usman ya ce ‘yan bindigar sun tsere ne dauke da raunuka a tare da su.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: