Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai ya musanta zargin shirinsa na komawa jam’iyyar PDP.

Elrufai ya bayyana haka ne a tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabiji na Arise.

Sai dai ya ce zai iya ficewa daga jam’iyya APC matuƙar ta gaza magance rikicin cikin gida da take fuskanta.

Sannan zai iya komawa wata jam’iyyar amma ba PDP ba..

Dangane da ganawa da yake yi da wasu jam’iyyu , Elrufai ya ce hakan ba ya na nufin ya na shirin barin jam’iyyar APC ba..

A cewarsa, kasancewarsa cikin jam’iyyar APC ba ya na nufin ba zai yi hulda da abokansa da ke cikin wasu jam’iyyun ba.

Ya kuma musanta zargin shirinsa na komawa jam’iyyar SDP bayan ziyarar da ya kai helkwatarta.

A cewarsa, ziyarar da ya kaiwa abokinsa Shehu Gabam ba ya ba nufin shirinsa na komawa cikinta ba.

Elrufai ya ce zuwa yanzu bai yanke shawarar ficewa daga jam’iyya APC ba har sai dan ta gaza magance rikicin da ke cikinta

Leave a Reply

%d bloggers like this: