Ofishin Jakadancin Kasar Saudiyya a Najeriya ya bai’wa Gwamantin Jihar Kano da wasu Jihohin Arewacin Kasar nan kadan 1,250 na Dabino.

Kasar ta Saudiyya ta bayar da tallafin ne domin rabawa al’ummar Musulmi a Jihar da wasu Jihohin Kasar, a wani bangare na taimakon da ta saba bayarwa a duk shekara a watan Azumijn na Ramadan.
Bayar da tallafin Dabinon na daga cikin shirin ayyukan jin-kai da cibiyar Sarki Salman ke yi don tallafawa mabukata da kuma karfafa alakar Najeriya da Kasar ta Saudiyya.

Jakadan Kasar Saudiyya a Kano Khalil Admawy ya mika tallafin a jiya Juma’a wani taro da aka gudanar.
A wannan shekarar Kasar Saudiyya ta ware Tan 50 na dabino a rabawa a Jihar Kano da wasu Jihohin Kasar, baya ga tan 60 da aka aikewa da birnin tarayya Abuja.

Khalil ya kuma mika godiyarsa ga Sarki Salman bin Abdul’aziz da Yari Mai jiran Gado Muhammad Bin Salman bisa tallafawa al’ummar musulmi da suke yi.
