Ya ce cikin shekara biyu an samu cigaba a ɓangare, sannan ya jaddada aniyarsa ta kin sulhu da yan bindiga.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ce gwamnatin jihar ba ta amfana da komai daga ma’adanai da ake haka a jihar.


Gwamnatin tarayya ce dai ta dage takunkumin hana hakar ma’adinai a jihar a baya.
Sai dai gwamnatin ta bai wa jihar damar ganawa da masu zuba hannu jari da gwamnatin jihar don duba hanyoyin da za a bunkasa fannin.
Sai dai gwamnan ya ce a halin yanzu zu na kokarin janyo bangarorin da ke da alaƙa da fannin don ganin an bunkasa don habaka hanyoyin shigar kudade a jihar
Sai dai ya ce a halin yanzu babu ko naira da ke shiga asusun gwamnati da sunan haraji daga bangaren masu hakar ma’adinai wanda abin takaici ne.
Sai dai ya ce da zarar an samu masu zuba jari a bangaren zai haifar da da mai ido.
Dangane da batun matsalar tsaro a jihar,gwamna Lawal ya ce cikin shekaru biyu an samu cigaba mai yawa a jihar.
Ya ce tun bayan zamansa gwamna a jihar ya samar da yan sa kai a jihar waɗanda au ke aikin tabbatar da tsaro.
Sannan ya jaddada aniyarsa ta kin yin sulhu da yan bindiga, ya na mai cewar dukkan wanda ya shirya ajiye makamansa to a shirye yake da ya karbeshi.
