Connect with us

Labarai

Rundunar ƴan sanda a Kano sun sake ceto yaro ɗaya a Jihar Anambara

Published

on

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano kuma mataimakin sufeton ƴan sandan Najeriya Ahmed Iliyasu ne ya bayyana hakan.

Ya ce an ceto yro ɗaya a jijar Anambara wanda kuma yanzu haka yara goma aka kuɓutar cikin 47 da ake zargi an siyar da su a jihar.

Kamar yadda muka baku labari a baya, rundunar ƴan sandan jihar Kano ce ta fara aikin bankaɗo asirin mutanen da ke sace yara ƙanana da shekarunsu ba su haura goma ba.

Ana siyar da yaran ne don bautar da su tare da sauya musu addini, da farko dai an ceto yara tara bayan nan kuma aka sake ceto yaro ɗaya wanda aka sace daga Kano zuwa Anambara.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Za’a Sake Duba Kadarorin Gwamnati Da Ganduje Ya Siyar Ba Bisa Ka’ida Ba

Published

on

Kwamitin bincike da gwamnatin jihar Kano ta kafa ya bayyana matakin da zai dauka kan zargin badakalar da tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yi.

Kwamitin ya ce zai sake duba kan kadarorin da aka siyar da kuma karkatar da su ga wasu tsiraru na gwamnatin da ta gabata.

Shugaban kwamitin, Mai Shari’a, Farouk Adamu shi ya bayyana haka a jiya Litinin 29 ga watan Afrilu a Kano.

Farouk ya ce daga cikin aikin kwamitin shi ne sake duba kan siyar da filayen idi da wuraren tarihi da gidaje da kuma makabartu a birnin mallakin gwamnatin jihar.

Ya ce za su yi bincike ko akwai almundahana yayin gudanar da su da kuma hukunta waɗanda ke da hannu a ciki.

Har ila yau, Farouk ya ce ba a kafa kwamitin domin bita-da-kulli kan wani ba illa binciken gaskiya.

Alkalin ya ba da tabbaci ga al’umma cewa zai yi adalci yayin binciken Ganduje ba tare da nuna bambanci ba da sauran wadanda abin ya shafa.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Gombe Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Ruwa A Jihar

Published

on

Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi alkawarin magance matsalar ruwan sha a fadin garin cikin gaggawa.

 

Gwamnan ya yi bayanin ne biyo bayan karuwa da matsalar ruwan sha ya yi a kwaryar jihar Gombe.

 

Mai taimakawa gwmantin jihar a harkokin sadarwa Isma’ila Uba Misilli ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamnan ya damu matuka da halin da al’umma ke ciki.

 

Bayanai sun nuna cewa gwamna Inuwa Yahaya ya ce za a kawo karshen matsalar ruwan ne zuwa gobe Laraba, 1 ga watan Mayu.

 

Saboda haka ne ma ya umarci ma’aikatar samar da ruwan sha ta jihar da ta gaggauta daukan dukkan matakan da suka dace domin magance matsalar.

 

Gwamnatin ta koka a kan cewa matsalar ruwan ta faru ne sakamakon katsewar wutar lantarki bayan lalata layukan wuta a tsakanin Jos da Gombe.

Continue Reading

Labarai

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Yin Gwaji Kafin Aure

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da kafa dokar gwajin lafiya tsakanin ma’aurata kafin aure.

 

Sabuwar dokar za ta tilastawa duk wanda za su yi aure gwajin lafiya domin kaucewa yaɗuwar cututtuka da za su zama barazana ga al’umma.

 

Rahoton ya nuna cewa an sanya gwajin cutar kanjamau, ciwon hanta da sikila a matsayin gwaje-gwajen da suka zama wajibi kafin aure.

 

Majalisar ta zartar da dokar ne a jiya Litinin yayin zaman da ta yi wanda ya gabatar.

 

Shugaban majalisar, Ismail Falgore ya ce dokar ta zama wajibi a wannan lokaci inda aka samu yawaitar cututtuka masu barazana ga lafiyar al’umma da dama.

 

Shugaban masu rinjaye na Majalisar dokokin, Lawan Hussein, ya ce an samu yawaitar yaɗuwar cututtuka ta hanyar auratayya kuma saboda dakile matsalar ne suka kirkiro dokar.

 

Ya ce za a saurari gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, domin saka hannun kan dokar kafin ta fara aiki a fadin jihar.

 

Ana sa rai idan aka saka hannu kan dokar za ta kawo sauki a kan matsalar rashin lafiya da ake fuskanta bayan aure a jihar.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: